Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Najeriya Ta Amince Da Sabbin Kungiyoyin Jami’o’i Biyu

0 224

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba da takardar shedar rajista ga wasu sabbin kungiyoyi biyu da suka yi rajista a tsarin jami’o’in kasar.

 

 

Kungiyoyin biyu wato National Association of Medical and Dental Academics (NAMDA) da Congress of University Academics (CONUA), sun balle daga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

 

 

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja a madadin gwamnatin Najeriya.

 

 

Da yake jawabi ga malaman, Dokta Ngige ya yi kira ga kungiyoyin da su yi aiki tukuru a matsayinsu na kungiyoyin kwadago a fadin Jami’o’in kasar nan ba tare da fargabar tsoratar da wasu kungiyoyin da ake da su a tsarin Jami’o’in kasar nan ba.

 

 

Ya ce an aike da wasiku zuwa ga hukumomin tsaro, domin a basu duk wani hakki da aka bai wa sauran kungiyoyin, na taronsu, AGM da taron wakilai.

 

 

“Haka kuma aka yi wa dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati, ciki har da ofishin Akanta Janar na tarayya, domin a cire maku kudaden rajista daga tushe a ba ku”.

 

 

Da yake tunawa da al’amuran da suka haifar da kungiyoyin biyu, Ngige ya ce kungiyar malaman jami’o’in sun nemi ma’aikatar kwadago a shekarar 2018 ta yi musu rijista a matsayin ‘Congress of Nigeria Academics’ da ma’aikatar ta kafa kwamiti, wanda ya yi aikin shi kafin farkon 2019, ya ba da shawarar cewa ya kamata a yi wa kungiyar rajista.

 

 

“Duk da haka, ba mu yi wa kungiyar rijista ba saboda muna son mu tabbatar da cewa muna kan turba mai kyau.

 

 

 

“A shekarar 2020 wannan bukata ta dawo kuma a wannan karon sun bayyana cewa an kore su daga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) don haka aka hana su kariya. Kuma cewa korar ta faru ne sakamakon rashin amincewarsu da bin hanyar ASUU.

 

 

“Sun koka da rashin tabbatar da dimokuradiyya a cikin ASUU da kuma rashin gaskiya a tafiyar da harkokin kudi na ASUU, kamar yadda ma’aikatar ta nuna wa ASUU cewa ba ta binciki asusun ta.

 

 

“Ya zuwa lokacin da suke fadin haka a shekarar 2020, ASUU ba ta yi bincike a asusun ta ba tsawon shekaru hudu”, in ji Ministan.

 

 

 

Da yake karin haske kan matsayin gwamnati na yi wa NAMDA rijista, Ngige ya ce likitocin da ke cikin malaman jami’o’i da suka hada da malaman makarantun gaba da aikin jinya sun koka da cewa ASUU ba ta basu kariya ba inda suka nemi a yi musu rajista a matsayin kungiya.

 

A cewar shi, malaman likitocin sun ce tattaunawar ASUU ba ta shafe su ba, ta fuskar jin dadin su, yanayin hidima da alawus-alawus.

 

 

 

Ya ce an kafa wani kwamiti da zai binciki korafe-korafen da gwamnati ta ga akwai bukatar ta daidaita wasu batutuwan da ake ta cece-kuce da su sannan ta yi amfani da shawarwarin kwamitin na cewa sun fito daga ASUU su samu kungiyarsu.

 

 

“Wannan ba wani abu ba ne. Mun warware kungiyar ’yan fansho ta Najeriya a shekarar 2018. Yanzu muna da ’yan fansho da ke ba da gudunmawa a ma’aikatun gwamnat,” in ji shi.

 

 

Da yake karbar takardar shaidar a madadin mambobinsa, Shugaban CONUA na kasa, Dokta Niyi Sunmonu, ya ce “da wannan cikakkiyar rajistar, muna tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za mu fara tattaunawa mai ma’ana tare da gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a kan yadda za mu iya samun kyakkyawar ma’amala ga malaman Jami’o’i da kuma ingantaccen aiki na dukkan tsarin ba tare da girgizawa da nutsewa cikin jirgin ba.”

 

 

 

Sai dai Dokta Sunmonu ya roki Ministan da ya sa baki a kan cece-kucen da ake yi na wanda ke karban cak din mambobin shi.

 

 

Da yake jawabi , shugaban NAMDA, Dr. Nosa Orhua wanda mataimakin shugaban ta na farko, Dr Ali Ramat ya wakilta, ya yaba wa Ministan bisa gabatar da takardun shaida tare da yin alkawarin cewa “ba za a sake rufe tsarin gaba daya ba”.

 

 

Duka CONUA da NAMDA sun nemi Ministan ya shiga tsakani wajen samun albashin mambobinsu na watanni takwas da suka ce ba sa cikin yajin aikin ASUU na wancan lokacin.

 

Shirin yi wa kungiyoyin rijistar kuma ya fara ne watanni uku da suka gabata a lokacin da kungiyar malaman jami’o’in ASUU ta dauki tsawon watanni 8 ana gudanar da harkokin ilimi a jami’o’in Najeriya.

 

 

 

Kasancewar wasu kungiyoyi biyu a cikin tsarin Jami’o’in banda ASUU, masu ruwa da tsaki a harkar sun yi imanin cewa gwamnati ta datse fika-fikan ASUU yadda ya kamata, kuma a karshe ta karya lagon ta a Jami’o’in Najeriya.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *