Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a sako mata da aka sace a Burkina Faso

Maimuna Kassim Tukur,Abuja.

0 47

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da Faransa sun yi kira da a sako mata da dama da aka yi garkuwa da su a lardin Soum da ke arewacin kasar Burkina Faso a tsakanin ranakun 12 zuwa 13 ga watan Janairu ba tare da wani sharadi ba.

 

 

Babban Kwamishinan Kare Hakkokin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk ya ce ya ‘firgita’ da sace-sacen da aka yi a “harrin farko na irin wannan da aka yi wa mata da gangan” a Burkina Faso.

 

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce ta damu matuka.

 

 

“Wadanda aka sace dole ne a mayar da su lafiya ga ‘yan uwansu cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba, kuma wadanda suka aikata laifin ya kamata a hukunta su gwargwadon yadda doka ta tanada,” in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price.

 

 

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Faransa ta yi Allah wadai da sace matan tare da yin kira da a gaggauta sakin matan.

 

 

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta ce tana da hannu wajen yin garkuwa da mutanen amma an yi garkuwa da mutanen ne a yankin da ‘yan ta’addan ke kai hare-hare.

Leave A Reply

Your email address will not be published.