Take a fresh look at your lifestyle.

Mali Ta Samu Karin Jiragen Yaki Daga Rasha

Aisha Yahaya, Lagos

0 15

Sarakunan sojojin Mali sun sami karin jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu daga kasar Rasha, na baya-bayan nan a jerin kayayyakin da sabbin manyan jami’an soja da kawayenta na siyasa ke kaiwa.

 

 

 

An kidaya jirage takwas da jirage masu saukar ungulu guda biyu a wani bikin da jakadan Rasha Igor Gromyko da shugaban mulkin sojan Mali, Kanar Assimi Goita suka halarta.

 

 

 

Rundunar sojan Mali ta ce kayan da aka yi jigilar sun hada da jiragen harin Sukhoi Su-25 da aka kera don tallafawa sojojin kasa; da Albatros L-39 da aka kera daga Czech.

 

 

 

Shi kuwa L-39, an kera su ne da farko don bada  horo da kuma amfani da su a wajen kai nhare-hare .

 

 

 

Har ila yau, Bamako ya karbi Mi-8s, wani jirgin sama mai saukar ungulu na jigilar kayayyaki kirar Rasha wanda Tarayyar Soviet ta kera wanda kuma ake jigilar sojoji da kayan yaki don kare sojojin kasa.

 

 

 

Jami’an kasar Mali ba su bayar da cikakken bayani kan ko nawa ne aka sayo kowane jirgin ba, kuma yayin da suka ce sun sayi makama, amma babu wani Karin bayani akan cinikayyar.

 

 

 

Wannan shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin isar da kayan aikin soja irin na Rasha, kari daga wadanda tuni aka tura cikin watannin Maris da Agusta, 2022.

 

 

 

Tun shekara ta 2012 Kasar da ke yammacin Afirka na fama da rikicin ‘yan jihadi da kuma rikicin siyasa da na bil adama.

 

 

 

Bayan da Kanal din da ke kan karagar mulki a halin yanzu suka yi juyin mulki a shekarar 2020, nan da nan dangantaka ta wargaje da tsohuwar mulkin mallaka Faransa, kuma Rasha ta shiga cikin wannan hali.

 

 

 

Majiyoyi da dama sun ce gwamnatin mulkin sojan ta fara shigo da jami’an tsaro daga kungiyar Wagner ta Rasha tun daga karshen shekarar 2021, lamarin da ya janyo suka daga kasashe da dama.

 

 

 

Hukumomin sojan dai sun musanta zargin, sun sanar da cewa sun farfado da alaka da Rasha da sojojinta ne.

 

 

 

Har ila yau, ta ce yanzu tana kai farmakin zuwa ga masu jihadi da ke fafutuka a kasar, da’awar da kwararrun soji ke tafkawa.

 

 

 

A wajen bikin, babban hafsan sojojin saman Mali na yanzu Janar Alou Boi Diarra ya yaba da sabbin kayayyakin a matsayin mataki na baya-bayan nan “na zamani da ba a taba ganin irinsa ba” na sojojin kasar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.