Take a fresh look at your lifestyle.

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Gargadi Manoma Akan Kona Daji

Aisha Yahaya, Lagos

0 15

Masu ruwa da tsaki a jihar Ogun, sun yi gargadi ga manoman yankin kan yadda ake kona daji. Gargadin dai na faruwa ne don sakamakon gobarar da ta barke a gonakin noma a baya-bayan nan, inda aka yi asarar miliyoyin naira.

 

 

 

Wannan lamari na baya-bayan nan ya faru ne, a makon da ya gabata a wata mummunar gobara da ta lalata wata gona mai fadin hekta 10 a kusa da Onipepeye, kan titin Abeokuta-Siun-Sagamu, a karamar hukumar Obafemi-Owode, jihar Ogun.

 

 

 

Gonar, mallakin tsohuwar jakadan Najeriya a Zambia/Malawi, kuma kwamishiniyar harkokin mata a jihar, Barr. Folake-Marcus-Bello ta yi asarar miliyoyin Naira, yayin da sama da itatuwan dabino 500, da sauran amfanin gonakin da aka shirya girbi suka lalace.

 

 

 

Shugaban manoma (Baale Agbe) a yankin Imeko, jihar Ogun, Cif Abdulazeez Ismail Abolore, wanda ya bayyana cewa an samu aukuwar irin haka a shekarar da ta gabata, ya gargadi manoman da su daina irin wannan hali.

 

 

 

“Mun fara yakin kamfen da wayar wa da mutane akan a yankinmu,  kuma muna gargadin manoma da masu  mafarauta da matasa da suke shiga kone-konen daji. Mafi yawan lokuta gobarar ta kan kauracewa sarrafawa, tana lalata amfanin gona da sauran kayayyaki masu daraja.

 

 

 

“Mun kuma horar da manoma don tabbatar da cewa iyakokin gonakinsu sun ciccibe ciyawa, ta yadda idan aka samu barkewar gobarar da ba a yi tsammani ba, zai yi wuya gonar ta kama wuta.”

 

 

 

KU KARANTA KUMA: Edo ta wayar da kan jama’a game da saran sare itatuwa ba bisa ka’ida ba, kona daji

Leave A Reply

Your email address will not be published.