Take a fresh look at your lifestyle.

2023: Dan Takarar Gwamna Na NNPP Na Nasarawa Ya Ci Gaba Da Yakin Neman Zabe A Karkara

0 14

Dan takarar gwamnan jihar New Nigeria People Party (NNPP), Mista Abdullahi Maidoya ya ci gaba da yakin neman zabe a shiyyar Nasarawa ta Yamma da ke jihar.

 

 

Maidoya ya ce yakin neman zaben jam’iyyar sa na kasa ya shirya ne domin samun nasara a zaben da za a yi a watan gobe.

 

 

A lokacin da yake jawabi ga dimbin jama’a, a yankin raya Umaisha da ke karamar hukumar Toto ta jihar, Abdullahi Maidoya ya yi alkawarin ba mata mata masu juna biyu kyauta, da kuma ba da ilimi mai araha idan aka ba su.

 

Maidoya ya bukaci al’ummar yankin da su zabi jam’iyyar NNPP daga sama har kasa domin inganta rayuwarsu.

 

 

“Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarmu, Injiniya Rabi’u Musa Kwankoso mutum ne mai gaskiya da aka gwada masa kuma aka amince da shi lokacin yana gwamnan jihar Kano.

 

Maidoya ya kuma yi kira ga masu zabe da su yi amfani da damar da INEC ta ba su, wato karin wa’adin katin zabe na dindindin (PVCs) domin karbar katin zabe a matsayin makamin daya tilo na zaben shugabannin da suke so.

Leave A Reply

Your email address will not be published.