Take a fresh look at your lifestyle.

Kotu ta daure tsohon ministan Rwanda da laifin cin hanci da rashawa

0 11

Wata babbar kotu a kasar Rwanda ta yanke wa wani tsohon ministan matasa da al’adu daurin shekaru biyar a gidan yari bisa samunsa da laifin cin hanci da rashawa, inda ta tsawaita hukuncin da aka yanke masa a baya da shekara guda.

 

 

Rahoton ya ce hukuncin da aka yanke a shekarar da ta gabata, kan Edouard Bamporiki, wani lamari ne da ba kasafai ake samun wani babban jami’in da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a kasar ba.

 

 

A watan Mayun da ya gabata ne aka dakatar da shi daga mukaminsa na majalisar ministocin kuma aka daure shi a gidan yari yayin da ake bincikensa da laifin almundahana da yin amfani da mulki.

 

 

Rahoton ya ce ya kasance a gidan kaso har zuwa lokacin da aka yanke hukuncin.

 

 

A halin da ake ciki, Bamporiki ya amince da tuhumar da ake masa a shafinsa na Twitter, ya kuma roki shugaba Paul Kagame da ya gafarta masa, amma a watan Satumba wata kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru hudu inda ya daukaka kara.

 

 

 

A ranar Litinin, wani alkalin babbar kotu a Kigali babban birnin kasar, ya ce “yana bukatar a yi adalci domin a ba da misali.”

 

 

Mawakin mai shekaru 39 da haihuwa kuma mai shirya fina-finai a baya ya kasance babban mai goyon bayan shugaba Kagame da jam’iyya mai mulki kuma ya yi fice cikin sauri.

 

 

Lauyan sa, Evode Kayitana, ya ce ba su yanke shawara kan ko za su daukaka kara ba.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.