Gwamnan jihar Kwara, Mallam Abdulrahman Abdulrazak ya amince da ayyana ranar Laraba 25 ga watan Janairu a matsayin ranar kyauta ga ma’aikatan jihar.
Sanarwar na kunshe ne a wata sanarwa da shugabar ma’aikatan jihar, Mrs Susan Oluwole ta fitar.
Wannan dai shi ne a bai wa ma’aikata isasshen lokaci domin samun katin zabe na dindindin daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin ba su damar taka rawa sosai a babban zabe mai zuwa.
Ana gargadin duk wadanda har yanzu basu samu katin zabe ba da su gaggauta yin hakan kafin cikar ranar tattarawa.