Take a fresh look at your lifestyle.

Sababbin Naira: Ƙungiya Zata Sanya Ido Ga Bankuna Ko Sun Bi Umarnin CBN

0 219

Wata kungiyar farar hula, Mai fafutukar ganin an samu daidaito ta Najeriya (NACOISED) ta ce za ta fara sanya ido kan yadda bankunan ajiya ke bin umarnin da babban bankin Najeriya CBN ya ba su na fitar da sabbin takardun kudi na Naira 200, 500 da 1000 kawai.

 

 

Ko’odinetan ta, Azor ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Awka, jihar Anambra.

 

 

Ya bayyana cewa kungiyar ta lura cewa wasu bankunan ba sa bin umarnin CBN kuma hakan ya haifar da firgici da fargaba a tsakanin ‘yan kasar.

 

“Bisa la’akari da yadda hukumomin CBN suka sha alwashin ba za su kara wa’adin ba, ‘yan kasar na shiga cikin damuwa da fargaba.

 

 

“Tunda yawancin al’ummomin karkara ba su da banki ko ATMs don raba sabbin takardun kudi, za ku iya tunanin makomar da ke jiran irin wadannan ‘yan kasa da har yanzu suna da tsofaffin takardun kudi a hannunsu, zuwa ranar 31 ga Janairu, 2023,” in ji shi.

 

 

Kungiyar ta yi alkawarin ci gaba da atisayen har sai ’yan kasar da abin ya shafa sun yi nasarar musanya tsofaffin kudaden Naira da sababbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *