Take a fresh look at your lifestyle.

Jihar Katsina Za Ta Karbi Bakoncin Shugaba Buhari

0 203

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya ranar Alhamis.

 

A yayin ziyarar shugaban na Najeriya zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Aminu Masari ta aiwatar.

 

Manyan ayyuka sun hada da Kofar Kaura Underpass, Kofar Kaura Water Works, Katsina State Internal Revenue House, Meteorological Institute, Darma Rice Mill, Batagarawa da Babban Asibitin Jihar Katsina da dai sauransu.

 

Ayyukan sun bazu a cikin Gundumomin Sanata guda uku na jihar.

 

A ranar Laraba ne gwamnatin jihar ta ayyana ranakun Alhamis 26 da Juma’a 27 ga watan Janairu a matsayin ranakun hutu don baiwa al’ummar jihar damar yiwa shugaba Buhari maraba, wanda dan jihar Katsina ne.

 

Shugaban ya isa jihar ne a daren Laraba daga Dakar Senegal, inda ya halarci taron noma na Darkar karo na biyu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.