Take a fresh look at your lifestyle.

NYSC TA NADA SABON KAKAKIN TA

0 171

Hukumar Yima kasa hidima ta kasa, NYSC, ta nasa sabon jami’in hulda da manema labarai da Jama’a Mr.Eddy Megwa a mukamin Darakta n.a. Hukumar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Mataimakin Daraktan hulda da Jama’a da manema labarai ya sanya wa hannu, Mr. Emeka Mgbemena ga manema labarai a Abuja babban birnin Tarayya
 
A shekarar 1989 Mr Megwa, ya kammala karatun Digirin shi a iLori daga bisani a shekarar 1990 ya kama aiki da hukumar NYSC a matsayin jami’in yada labarai bayan yiwa kasa hidimaa.
 
Sabon Jami’in yana da cikakken kwarewar aiki, kuma bayada nuna bambancin kabila kuma yayi tafiye-tafiye zuwa kasashe har da kwasa-kwasai a gida da wajen Najeriya.
 
Yayi aiki a sakateriyar NYSC dake jihohin Ribas,Anambara, Yobe, Borno, Barno da Benuwai a matsayin Jami’in hulda da Jama’a .
 
A shekara ta 2019, aka nada shi jami’in hada kan hukumar NYSC a jihar kuros riba, sai a shekara ta 2020 aka maida shi sakatariyar NYSC ta Legas.
 
Wannan sabon mukamin nashi zai bada damar nuna irin kwarewar aiki da yake da shi a bangaren hulda da Jama’a.

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *