Jami’an ‘yan sanda da na gwamnati sun ce wani bam mai karfi ya tashi a ranar Litinin a kusa da wani masallaci da ofisoshin ‘yan sanda a birnin Peshawar da ke arewa maso yammacin Pakistan, inda ya kashe akalla mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.
Fashewar ta faru ne a masallacin da mutane da dama suka taru domin yin addu’a, kamar yadda jami’in ‘yan sanda Sikandar Khan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Litinin. Khan ya kara da cewa
“Wani bangare na ginin ya ruguje, kuma ana kyautata zaton mutane da dama na karkashinsa.”
Mohammad Asim, mai magana da yawun asibitin Lady Reading da ke Peshawar, ya ce sun karbi mutane 90 da suka jikkata, wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali. Wakilin Al Jazeera, Kamal Hyder daga Islamabad ya ce an samu cikakkun bayanai cewa wani dan kunar bakin wake ne ya kai harin.
“Muna kuma samun cikakkun bayanai… dan kunar bakin waken da kansa yana zaune a layin farko na sallar jam’i a cikin masallacin,” in ji shi.
Comments are closed.