Take a fresh look at your lifestyle.

SHUGABA BUHARI YA KADDAMAR DA RUKUNIN GIDAJE NA KASA

0 200

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da Shirin samar da gidaje a fadin kasar.

Karkashin Maaikatar aiyyuka da gidaje ta tarayya,gwamnati ta gina rukunin gidaje  34 karkashin Shirin a babban birnin tarayya Abuja.

Kama yanzu, Gwamnatin tarayya ta gina gidaje a jihohin Kaduna, Kogi, Delta, Imo, Osun, Nasarawa, Niger, Jigawa da Edo.

Ana sa ran Shugaban kasa zai kuma kaddamar da Karin wasu gine ginen gidajen nan gaba.

Da yake kaddamar da rukunin gidaje 68 a jihar Edo, Shugaban yace: A yau na kaddamar da wadannan rukunin gidaje domin cika alkawuran da nayi na kawo sauyi.”

Ministan Kiwon Lafiya na kasa, Dr. Osagie Ehanire wanda ya wakilci shugaban kasa yace an gina arukunin gidaje a jihohi 34 a fadin kasar sakamakon daya daga cikin alkawuran da gwamnati mai ci yanzu tayi domin kyautata rayuwar ‘yan Najeriya.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *