Take a fresh look at your lifestyle.

MATAN ZIMBABAWE SUN SHIGA HAKAR MAADININ AQUAMARINE

0 221

Karo na farko irin shi a Afirka Zimbabwe ta dauki mata aikin hakar maadinai.

A kusa da garin Karoi, kimanin kilomita 200 arewa maso gabashin babban birnin Zimababwe Harare na sauya rayukan mata a wannan .

Zimbaqua na samar da aiyyukan yi tare da canza rayukan mata a wannan yanki,wadanda akasarin su basu da aikin yi. “Iyalai na suna cikin wani hali na kuncin talauci kafin in shiga aikin hakar maadinai,” a cewar Sylvia Mugova, maaikaciyar hakar maadinai kuma uwar ‘ya’ya biyar. koda yaushe makaranta na koro Yara na saboda rashin kudin makaranta. Miji na baya da akin yii. Kuma mune ke kula da suruka ta. Duk burina shine in ciyar da iyalai na kuma hakar Maadinai ya biya mani bukatu na.”

Kamar sauran mata da basuyi makaranta ba, Mugova na daga cikin mata 35 da Zimbabwe ta dauka aiki.

Kimanin kashi goma sha biyar cikin dari na mata sama da Miliyan Bakwai dake kasar suna kananan masanaantu da aikin hakar maadini.

Mahakan na hakar fadin fili mai Hkta 50 inda ake hakar Maadinin aquamarine, sunan da suke kiran shi saboda darajar shi a kasuwar duniya.

Wajen mata gagarumin aikin karfi ne saboda anfani da Hamma mai nauyin kilogram 12 zuwa sha shida,kuma an horas da su yadda zasu fasa dutsen,daga karshe a basu albashin kasa da dala $300 a wata.

Wanna aikin karfi Maza ne akafi sani da gudanar da shi , dutsen kuwa a tura shi zuwa birnin Bangkok domin gyara da sarrafa shi.

Kamar yadda manajan wajen hakar Rumbidzai Gwinji yace Zimbabwe ta bullo da wani sabon salo na hakar Maadini. Wannan  gagarumin aiki na taimakawa aluma wajen samar da hanyoyin shawo kan matsalolin mata. Yanzu mata basu dogara akan sai mazajen su sun kawo musu kayan masarufi ba. Ga matan da basuda mazaje amma na kula da yara, ba zasu taba samun hanyar da tafi wannan kyau ba wajen samun kudade. Suna kula da ‘ya’ya, bukatun makaranta da ciyar da su’yanzu basu da matsalar kudi,” inji ta.

A halin yanzu kanfanin na fitar da Maadinin ta zuwa kasashen Indiya da Thailand; ta samar da wasu hanyoyi na anfani da maadinin aquamarine da matan kasar ke hakowa.

Muna matukar murnar sayar da maadinin da aka sarrafa zuwa kasashen waje. Fatan mu a nan shine samar da damarmaki ga mata a kasar,” Inji Zindoga.

africanews

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *