Take a fresh look at your lifestyle.

Zaben 2023: Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa Ya Nemi Kuri’a A Jihar Neja

Aliyu Bello Mohammed, Katsina

0 189

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zabi ‘yan takarar jam’iyyar a kowane mataki a babban zaben da za a yi na bana domin bunkasa ci gaban Nijeriya cikin sauri.

Sanata Abdullahi Adamu ya yi wannan roko ne a yayin babban gangamin jam’iyyar APC a yankin Bida a jihar Neja yayin da yake gabatar da tutocin jam’iyyar APC ga daukacin ‘yan takara na shiyyar A daga ‘yan takarar gwamna, Sanata da na wakilai.

Adamu ya ci gaba da cewa APC babbar jam’iyyar siyasa ce da za ta iya lashe zabe mai zuwa.

Ya kuma tabbatar wa ‘yan kasar cewa jam’iyyar za ta ciyar da Najeriya gaba.

“Kuri’ar dan takarar shugaban kasa Sanata Bola Ahmed Tinubu da dan takarar mataimakin shugaban kasa, Shettima da kuma dan takarar gwamnan jihar Umar Bago da abokin takararsa, Kwamared Yakubu Garba da sauran mukamai na zabe ne na tsaro,” Adamu ya ce.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya samu wakilcin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa a yankin arewa ta tsakiya, Alhaji Muazu Bawa.

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Bello a lokacin da yake gabatar da ’yan takarar jam’iyyar APC ga dimbin jama’ar da suka taru a Bida, ya ce akasarin su an jarraba su kuma an amince da su don haka ya shawarci ‘yan Neja da su zabi APC gaba daya domin cimma burin da ake so na ciyar da jihar gaba.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Alhaji Haliru Zakari Jikantoro da babban daraktan yakin neman zaben Umar Bago, Alhaji Isa Sidi Rijau a nasu jawabansu sun shawarci ‘yan Neja da su yi tunanin zaben duk ‘yan takarar jam’iyyar APC bisa la’akari da nasarorin da suka samu.

Shima da yake nasa jawabin, Shugaban kungiyar Makiyaya, Janar MA Garba wanda ya yi magana a madadin dattawan shiyyar A, ya ce a shirye suke su marawa dukkan ‘yan takarar jam’iyyar APC goyon baya tun daga kasa har zuwa jihohi domin samun nasarar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *