Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya Ya Haramta Sayar Da Takardun Naira

Aisha Yahaya, Lagos

0 218

Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP, Usman Alkali, ya bayar da umarnin aiwatar da cikakken dokar  babban bankin Najeriya, CBN, ta shekarar 2007, wadda ta haramta safara da sayar da takardun Naira.

 

 

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a  ranar Juma’a a Abuja.

 

 

 

Ya ba da umarnin kamawa tare da gurfanar da duk wadanda ke da hannu wajen sayar da kudaden Naira tare da gurfanar da su gaban kuliya.

 

 

 

Adejobi ya ce wannan umarni ya yi daidai da tanadin sashe na 20 da 21 na dokar CBN na shekarar 2007 daya shafi aikata laifuka da suka hada da sata, ko sayarwa ko kuma yin ciniki a kan takardar Naira.

 

 

 

Ya umurci dukkan mataimakan sufeto-Janar na ‘yan sanda da kwamishinonin ‘yan sanda masu kula da oda da tsare-tsare da su aiwatar da cikakken aikin su.

 

 

 

IGP din ya kuma ba da umarnin sanya jami’ai da maza na sashen binciken manyan laifuka na rundunar da kuma hukumar leken asiri ta rundunar a cikin shirin ko ta kwana.

 

 

 

A cewarsa, wannan umarni na ci gaba ne ga manufofin gwamnatin Najeriya da yunkurin tabbatar da tanade-tanaden dokar CBN, 2007 da kuma daukaka darajar kudin Najeriya.

 

 

 

Ya nanata wa’adin rundunar ‘yan sandan da su tabbatar da duk wasu dokoki da ka’idoji ba tare da la’akari da yadda wasu hukumomin tsaro suka amince da su ba.

 

 

Alkali ya yi kira ga jama’a da su baiwa rundunar ‘yan sandan hadin kai wajen tabbatar da dokar CBN kan masu karya doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *