Wata yarinya ‘yar shekara 10 ‘yar kasar China, WEI/YUE CHEN, ta ba da gudummawar kayan abinci ga gidan marayu na yara da ke Abuja.
A lokacin da take gabatar da kayayyakin ga gidan marayun,Yarinyae ta bayyana tallafin a matsayin karamar hanyarta ta taimaka wa yara marasa galihu da ba da gudummawarsu don samun lafiya da farin ciki.
Ta bayyana cewa wannan ne karon farko da ta ba da gudummawa ga gidan marayu sannan ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan jin kai don yin tasiri ga marasa galihu a cikin al’umma.
“Ina son yaran su kasance cikin koshin lafiya da farin ciki kuma ko da yake wannan ne karo na farko da na ba da gudummawa ga gidan marayu, na yanke shawarar cewa zan ba da gudummawa kowace shekara ga marasa galihu don taimaka musu ta rayuwa”, in ji ta.
Yarinyar ‘yar shekara 10 ta ci gaba da bayyana cewa, tallafin an yi shi ne domin karfafa wa yara gwiwa don kokarin ganin sun je makaranta da kuma rayuwa cikin koshin lafiya ta yadda za su samu Kyakyawar rayuwa.
Mahaifinta, WEI/YAN BIN da mahaifiyarta HAN/TING TING, masu kamfanin Heavy Duty Machinery da Engineering Nigeria Limited na daga cikin masu kai ziyara gidan marayun.
A cewar mahaifiyarta, yarinyar ta zo Najeriya ne tun ba ta wuce shekara daya ba kuma ta bar kasar Sin tana da shekaru hudu.
Ta ce ta dawo Najeriya ne bayan hutun da ta yi, kuma a lokacin bikin cikar ta shekaru 10 da haihuwa, ta yanke shawarar yin amfani da kudin aljihunta wajen bayar da gudummawar rayuwar yaran saannin ta da kuma wadanda suka girme ta.
Leave a Reply