Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar zartaswar Najeriya ta amince da naira biliyan 117 na kayan tarihin mai

0 228

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da kashe Naira biliyan 117 domin gina gidan tarihin mai na Oloibiri a jihar Bayelsa da ke Kudancin Najeriya.

 

 

Ministan kasa na Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen taron majalisar na ranar Laraba, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

 

 

Sylva ya ce gidan kayan gargajiyar da aka tsara zai kuma zama cibiyar bincike da inganta harkokin ilimi.

 

 

“Majalisar zartaswa ta tarayya a yau ta amince da bayar da kwangilar gina gidan adana kayan tarihi da cibiyar bincike na Oloibiri ga Julius Berger PLC a kan kudi naira biliyan 117 nan da  watanni 30,” inji shi.

 

 

Ministan ya bayyana cewa tun a farkon shekaru 80 na Marigayi Shehu Shagari aka fara aiki,amma ba a iya ci gaba da aikin ba saboda karancin kudi, amma gwamnatin Muhammadu Buhari ta dukufa wajen ganin anci nasara saboda muhimmancinsa.

 

 

Dangane da layukan da ake samu a gidajen man fetur a fadin kasar nan, Ministan ya ce wasu ‘yan kasuwa ne ke da alhaki saboda suna son cin kazamar riba, amma gwamnati za ta yi duk abunda ya dace don ganin an daidaita lamarin.

 

 

Ya ce: “Wannan abin takaici ne kuma ba ma jin daɗin abin da ke faruwa ko kaɗan. Kowa ya sanya akan irin wuce gona da iri na waɗannan ‘yan kasuwa. A halin yanzu ana samun wadatuwa amma abin takaici muna fuskantar wasu matsaloli wajen rarrabawa da jigilar kayan zuwa wurare daban-daban. Ina so in tabbatar muku cewa ana yin komai; Hukumar NNPC da sauran masu ruwa da tsaki suna aiki tukuru don ganin an shawo kan wannan matsala.

 

 

“Muna da rahoton samun riba daga ‘yan kasuwa kuma na umurci hukumar kula da farashin kayayyaki, Nigerian Midstream da Downstream Hukumar Kula da Man Fetur da su sanya takunkumi ga duk wanda ya ci riba a irin wannan yanayin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *