Take a fresh look at your lifestyle.

Mikel da Okocha sun Aika Sakon Alkhairi ga wadanda girgizar kasar Turkiyya ta shafa

Theresa Peter,Abuja.

0 152

Tsoffin ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya, Austin Okocha da Mikel Obi sun bi sahun sauran mashahuran mutane wajen aika sakon fatan alheri ga wadanda girgizar kasar Turkiyya ta shafa.

 

 

 

A yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan bayar da agaji da tallafi ga Turkiyya bayan mummunar girgizar kasa da ta afku a kasar da kuma Siriya da sanyin safiyar Litinin, ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya Austin Okocha da Mikel Obi mai ritaya suma sun bi sahun wadanda ke alhinin Bala’in da ya shafi kasashen biyu.

 

 

Girgizar kasa mai karfin awo 7.8 ta afku a Turkiyya a ranar litinin, mafi muni da aka taba fuskanta cikin shekaru sama da 100 a kasar.

 

 

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a lokacin da yake magana a lardin Hatay dake kusa da cibiyar girgizar kasar ,ya ce adadin mutanen da aka tabbatar sun mutu a Turkiyya ya karu zuwa 9,057.

 

 

 

Jami’an Sham da kungiyar ceto a yankin arewa maso yammacin Sham da ke hannun ‘yan tawaye sun kuma ce adadin wadanda suka mutu a can ya kai 2,662, wanda ya kawo adadin zuwa 11,719.

 

 

 

Yayin da bala’in ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 11,719, da dama sun jikkata, yayin da wasu da dama ke karkashin baraguzan gine-gine da suka ruguje.

 

 

 

Daga cikin wadanda suka jikkata har da Ahmet Eyup Turkaslan, mai tsaron gidan kwalon kafa ta Turkiyya.

 

 

Tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea, Mikel, wanda shi ma ya taka leda a kasar Turkiyya a cikin magriba, a shafinsa na Instagram ya mika ta’aziyyar shi ga wadanda girgizar kasar ta shafa.

 

 

“Zuciyata ta baci ganin bidiyon girgizar kasa a Turkiyya jiya,” ya rubuta.

 

 

 “Ina mika sakon ta’aziyyata ga mutanen da suka rasa ‘yan uwansu a wannan mummunan lamari. Allah ya baku dukkan karfin halin jure rashin da ba za a iya maye gurbinsa ba.

 

 

Okocha ya kuma rubuta cewa, “Tunanina da addu’a na tare da daukacin al’ummar Turkiyya. Ta’aziyyata ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *