Gwamna Soludo Ya Nufi Ci gaban Tattalin Arziki Tare Da Fitar da Ƙasashen waje
Aliyu Bello Mohammed, Katsina
Gwamna Chukwuma Charles Soludo na jihar Anambra, ya yi hasashen cewa wurin da za a yi taron fitar da kayayyaki a yankin Dunukofia, zai inganta tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da aikin titin Igwe Ezechi Okoye mai tsawon kilomita 2.14 a garin Dunukofia na jihar Anambra.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Christian Aburime, Soludo ya fitar, ya jaddada cewa wurin taron ya hada da bayar da kadada dari (100) na fili da al’ummar yankin suka bayar.
Da yake magana kan titin Igwe Ezechi Okoye bayan ya duba aikin da ake yi, Gwamna Soludo ya bayyana gamsuwa da irin yadda aka gudanar da aikin ya zuwa yanzu.
A cewar Gwamnan, farashin filaye a wurin zai yi tashin gwauron zabi da zarar an kammala aikin, wanda hakan zai sa al’ummar Dunukofia su yi arziki.
Yayin da yake nuna godiya ga jama’a da suka ba su damar yin hidima, ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnatin sa na aiki ba dare ba rana domin ganin jihar ta zama wuri mai kyau ga kowa da kowa.
Leave a Reply