Take a fresh look at your lifestyle.

Jihar Kano: Jam’iyyar NNPP ta yi kira da a gudanar da bincike kan zargin siyan kuri’a

Yusuf Bala Nayaya, Kano

0 265

Dantakarar majalisar dattawa a Kano ta Kudu karkashin inuwar jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Abdulrahman Kawu Sumaila, yayi kira ga jami’an tsaro su zurfafa bincike kan zargin yunkurin siyan kuri’a a yankinsa na Kano ta Kudu.

Abdulrahman Kawu Sumaila wanda ya kasance tsohon mai ba wa Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan sha’anin majalisa kuma tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar Sumaila/Takai shi ya bayyana wannan kira a lokacin da yayi jawabi ga manema labarai a jihar Kano.

Yayi zargin cewa dan majalisa mai wakiltar wannan yanki kawo yanzu Sanata Kabiru Ibrahim Gaya na fakewa da gudanar da aikin ba da tallafi a yunkuri na siyan kuri’u al’ummar yankin.

“ Yayin da ya rage kwanaki kadan a gudanar da zabe Sanata Kabiu Gaya ya fara rarraba kudade ga masu kada kuri’a da sunan ba da tallafi.
An raba wa kimamnin mutane 1000 Naira 5000 kowanne daga kananan hukumomi da aka zaba.
Muna da kananan hukumomi 16 a wannan yanki , idan aka tattara adadin kudaden za a ga kimanin miliyan 80 kenan.
Ina kira ga hukumar ICPC da ta EFCC su gudanar da bincike kan wannan batu.
Sanata Gaya baya wakiltar yankin yadda ya dace. Nayi alkawari idan an zabe ni a matsayin Sanata zan samar da wakilci nagari a wannan yanki.”

“Mutanenmu sun gaji da irin wannan wakilci da dama sun rasa rayukansu a kan hanyar Kano zuwa Wudil zuwa Gaya dalilin rashin kyan wannan hanya.
Sama da shekaru 10 na wakilcin Sanata Gaya an gaza samar da gyara a wannan hanya don ganin an kare rayukan al’umma.” Inji Kawu Sumaila

Ya kara da cewa “Duk tsawon wadannan shekaru da Sanata Gaya ke wakiltar mutanen Kano ta Kudu ba a taba hada taron jin ra’ayin al’umma ba, wannan abun takaici nekuma alamu ne na rashin samun wakilci nagari.”

Dan takarar jam’iyyar ta NNPP a Kano ta Kudu ya jaddada cewa idan har yayi nasarar samun wakilcin al’umma zai samar da sauyi inda zai rika shirya tarukan jin ra’ayin al’umma.

A cewar Sumaila “ Na ziyarci mazabu a yankin Kano ta Kudu, na san bukatunsu, tuni ma mun fitar masu da tsare-tsare. Na yi alkawarin idan nayi nasara mutanenmu za su sha romon dimukuradiyya”.

 

AK

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *