Take a fresh look at your lifestyle.

Za’a yi Shari’ar ‘Yan Tawayen Sojojin Chadi da Suka Yi Sanadiyar Mutuwar Shugaban Kasar

0 140

Kasar Chadi za ta fara shari’ar ‘yan tawaye 150 da ake zargi da haddasa mutuwar shugaba Idriss Deby.

 

 

Za’ a gudanar da shari’ar ne a Kléssoum, a cikin wani babban gidan yari, kamar yadda wani kafar yanar gizo na labaran majiyoyin shari’a ya ruwaito.

 

 

Wadanda ake zargin suna cikin kungiyar Front for Concord and Change in Chad (FACT), kungiyar ‘yan tawayen da ta kaddamar da farmaki don hambarar da gwamnatin Chadi daga sansanonin ta na baya a Libya a shekarar 2021.

 

 

Ana tuhumar su da laifin ta’addanci, sanya yara aikin soja, sojan haya, zagon kasa ga tsaron kasa, da kuma kashe shugaban kasa mai ci.

 

 

An kashe Idriss Deby a fagen daga a watan Afrilun 2021 a lokacin da yake kula da ayyukan sojojin da ke fatattakar ‘yan tawaye.

 

 

Da taimakon Faransa, sabbin shugabannin sojan Chadi sun sami damar hana ‘yan tawayen ci gaba.

 

 

Kusan shekaru biyu da mutuwar Deby, tattaunawa tsakanin ƙungiyoyin ‘yan tawaye da gwamnatin Chadi ta ci tura.

 

 

Kungiyar ta kauracewa tattaunawar samar da zaman lafiya, inda ta bukaci a sako mambobin ta daga gidan yari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *