Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Jihar Neja Za Ta Gurfanar Da Mutanen Da Suka Ki Tsohuwar Naira

Aliyu Bello Mohammed, Katsina

0 181

Gwamnan jihar Neja dake arewa ta tsakiya a Najeriya, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya umurci hukumomin tsaro da su kamo mazauna jihar da ke kin amincewa da tsohuwar takardar Naira a fadin jihar.
A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Ahmed Ibrahim Matane ya fitar, ta bayyana cewa har yanzu akwai tsofaffin kudaden Naira na N1000, N500 da N200, kuma duk wanda ya ki karbar tsohon kudin a yi maganinsa kamar yadda doka ta tanada. .
Matane ya kara da cewa, “Ya zo ga gwamnati cewa wasu mutane da ‘yan kasuwa na kin amincewa da tsohon kudin Naira na ‘yan kasa, lamarin da ba shi da lafiya wanda hakan ya jawo wa al’ummar Jihar wahala.
Ya yi gargadin cewa har yanzu tsofaffin takardun Naira na nan daram kuma duk wanda aka samu yana kin su za a kama shi kuma a hukunta shi.
“Ina kira ga jama’a da su ci gaba da gudanar da sana’arsu ta halal, sannan su kai rahoton duk wanda ya ki karbar tsohuwar takardar Naira ga hukumomin tsaro domin daukar matakin da ya dace”.
Idan dai ba a manta ba a baya ne gwamnatin jihar ta shigar da kara a gaban gwamnatin tarayya kan manufar sauya fasalin Naira na babban bankin Najeriya CBN.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *