Hukumar kidiya ta NPC ta ayyana ‘yan Jaridu a matsayin wani tubali da Zai samar da nasara
Nura Muhammed,Minna.
Kwamishinan hukumar kidayar Jama’a NPC ta kasa mai kula da jihar Neja arewa ta tsakiyar Najeriya Alhaji Sunusi Yusuf shine ya wakilci Babban kwamishinan NPC, Alhaji Mahammadu Dattijo a wajen taron wayar da kai na yini guda da hukumar ta shiryawa manema labarai a garin Minna fadar gwamnatin jihar Neja.
Kwamishinan Wanda mai bashi shawara kan tsare tsare Alhaji Nda Ali Abdullahi ya wakilta ,yace “kiran da Zan yi wa alummar kasar shine su hada hannu da hukumar domin ganin an sami nasarar gudanar da ayyukan kidayar alumma da gidaje a fadin kasar”.
“nayi farin cikin ganin yadda gwamnati take bai wa ga hukumar da kuma ‘yan jaridu bisa irin namijin kokarin su na yada aikace aikace ga alummar Najeriya “.inji Kwamishinan
kwamishinan yace hukumar ta yi nisa wajan gudanar da shirye shiryen ta na ganin an yi kidayar bisa irin tsare tsaren da ta shafe shekaru tana yi don ganin an sami nasarar hakan a watan Maris da Afrilu na wannan shekarar da muke ciki.
A jawabin sa na maraba shugaban hukumar a jahar Neja Alhaji Nma Shehu Alhaji ya ce “ yan jaridu nada mihimmiyar rawa na ganin aikin ya tafi kamar yadda aka tsara.
Shugaban hukumar ya Kara da cewar ,”hukumar na bukatar ganin ‘Yan jaridun sun Kara himma wajan Kara yada manufofi da Kuma aikace aikacen hukumar NPC”.
An dai gabatar da mukala a Taron na yini daya, inda aka tabu batutuwa da suka hada da rawar da Yan jaridun zasu taka wajan ganin an Sami nasarar gudanar da ayyukan kidayar da za a fara tun daga ranar 29 ga watan Maris zuwa 3 ga watan Afrilu wannan shekarar ta 2023.
Cikin wadanda suka gabatar da mukala akwai professor Nicholas Iwakwagh na jami’ar fasaha ta gwamnati taraya dake Minna da Malam Bala Galadima na jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida Dake Lapai da Malam Sunusi Yusuf Wanda ma’aikacin hukumar kidaya ne a jahar Neja.
Yanzun kusan ma’aikatan wucin gadi sama da dubu saba’in ne zasu Yi aikin a jihar Neja.
Leave a Reply