Gwamnatin jihar Katsina ta shirya wani taron bita domin ilmantar da masu ruwa da tsaki hanyoyin inganta tsaro ta hanyar shigar da al’umma a cikin sha’anin tsaro da zaman lafiyar su wato Community Policing.
Taron bitar na wuni biyu hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jihar da hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya wato UNDP a takaice
A lokacin taron wanda ya gudana a birnin Katsina, mai baiwa gwamnan jihar Katsina shawara akan sha’anin tsaro Alhaji Ibrahim Katsina ya bayyana cewa shirya taron ya biyo bayan kulla wata hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da majalisar dinkin duniya domin tallafama kokarin gwamnatin jihar na magance matsalar tsaron da wasu yankunan ta ke fuskanta domin zaman lafiyar al’ummar jihar baki daya
Yace majalisar dinkin duniya tayi maraba da manhajar “Community Policing” da gwamnatin jihar Katsina ta bullo da ita, inda akan haka ne ta dauki nauyin gudanar da taron bitar na masu ruwa da tsakin domin cimma nasara wajen magance matsalar tsaron a fadin jihar
Ibrahim Katsina yace” Mun dauko shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautun gargajiya daga hakimai zuwa masu unguwanni da malaman addini da yansanda da kuma yan Vigilante yan sandan farin kaya da jami’an kula da Iyakokin kasa da dai sauran masu ruwa da tsaki akan tsaron al’umma daga fadin jihar nan domin yi masu bita akan yadda zasu yi aiki tare wajen tabbatar da tsaro a cikin al’umma.
“Muna sa ran idan aka inganta wannan tsari na Community Policing wanda har majalisar dinkin duniya ta gamsu da shi kuma kamar yadda muke ganin haske akan shi babu shakka idan aka kara samun hadin kai wajen aiki tare zamu kawo karshen wannan matsala ta tsaro da izinin Allah”, inji shi.
Abubuwan da suka gudana a wajen taron sun hada da gabatar da da kasidu daga bakin masana da kwararru akan tsaro da zamantakewar al’umma domin kara ilmantar da mahalartan hanyoyin hada kai domin inganta tsaro da zaman lafiyar al’umma
Ana kuma sa ran wadanda suka halarci taron zasu koma su ilmantar da abokan aikin su ilmin da suka samu domin cimma nasarar magance matsalar tsaron a fadin jihar ta Katsina
Leave a Reply