Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ke jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da shugabar ma’aikatan tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan.
Haka kuma akwai Ministocin Watsa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, Mai Shari’a, Abubakar Malami, Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital, Isa Pantami, Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Kasa, Zainab Ahmed, Babban Birnin Tarayya, Mohammed Bello da Ilimi, Adamu Adamu.
Sauran sun hada da Ministocin Lafiya, Dokta Osagie Ehanire, Harkokin jin kai, Gudanar da Bala’i da Ci gaban Jama’a, Sadiya Farouq, da kuma Ministocin Ma’aikatar Gona, Mustapha Shehuri, Kasafi da Tsare-tsare na Kasa Clement Agba da dai sauransu.
Leave a Reply