Take a fresh look at your lifestyle.

SULTAN NA SAKWATO YA TSAYAR DA 2 GA WATAN MAYU RANAR KARAMAR SALLAH

0 486

Sarkin Musulmi kuma Shugaban majalisar koli ta Musulmi , Muhammad Sa’ad Abubakar, ya amince da rahoto daga hannun Kwamitin amintattatu akan addini na tsayar da ranar Litinin 2 ga watan Mayu 2022 a matsayin ranar karamar Sallah .
Wannan sanarwar ta Frito me ta hannun Shugaban kwamitin kula da adding kuma wazirin SAKWATO,Farfesa Sambo Junaid ..
Sanarwar na cewa,kwamiti tare da hadin gyuiwar kwamitin duba wata basu samu wani rahoto na ganin sabon watan Shawwal na shekara ta 1443 AH a fadin kasar.
“kwamitocin tbiyu sun nemi bayanai daga bakin hukumomin duban wata a fadin kasar a ranar Asabat 30th ga watan Afrilu, 2022 wanda yayi dai dai da 29th na azumin Ramadan 1443 AH.
“Sultan ya amince da rahoton kwamitin na tsayar da ranar Litinin 2 ga watan Mayu 2022 ya zama bukin Sallah karama,”  a cewar shi.

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *