Dantakarar mataimakin shugaban kasa a jamiyyar Labour Party Sanata Datti Baba Ahmed ya bayyana karfin gwiwarsa na lashe zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 25 ga watan fabrairun 2023.
Sanata Datti ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wani taro da Kungiyar Dattawan Arewa ta shirya A Abuja, gabanin zaben 2023 dake tafe.
Dantakarar mataimakin shugaban kasar a jamiyyar Labour Party ya ce da shi da dantakatrar shugaban kasa na jamiyyar Peter Obi sun fi duka saurar abokan karawarsu na sauran jamiyyun da za a fafata da su cancanta ciki kuwa har da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da Atiku a Abubakar na jamiyyar PDP.
“cikin jam’iyyu 18 , sha biyar ba a ganinsu, cikin ukun da suka rage, guda biyu tsarinsu ya sabawa cin zabe a Najeria, sannan ya kuma sabawa tarihin siyasar Najeriya.” in Ji Baba Ahmed
Ya ce dalilin da ya sa Bola Ahmed Tinubu bai zama mataikamakin shugaban kasa a 2015 ba , babu yanda za a ayi wannan dalilin ya zama shugaban kasa a yanzu.
Ya kara da cewa “APC ba ta cikin lissafi, suna da kudin kashewa, su je su yi ta kashewa amma ba sa cikin lissafi, sannan PDP ma bata tsara kanta a yanda siyasar Najeriya ke tafiya ba, dan arewa ke mulki a yanzu , kuma yanzu lokaci ne da ya kamata mulki ya koma kudu”.
Datti Babba Ahmed ya ce jam’iyyar Labour Party ce kadai shi da Peter Obi suka fi dacewa a zaba sannan ya yi kira ga al’umma da su je su duba tarihin rayuwarsu don tabbatar da cancanatarsu.
AK
Leave a Reply