Take a fresh look at your lifestyle.

2023: Dan Takarar Shugaban Kasa na ZLP Yayi Alkawarin Gina Matatun Mai na Zamani

Aliyu Bello Mohammed

0 127

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Zenith Labour Party, ZLP, Mista Dan Nwanyanwu, ya yi alkawarin gina matatun mai a kowace shiyyar Najeriya ta Geo – Siyasa da kuma gyara matatun mai a kasar idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Mista Nwanyawu ya yi wannan alkawarin ne a yayin taron da aka yi a garin Lafia babban birnin jihar Nasarawa.

Ya ce idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta gyara matatun Kaduna, Warri, da Fatakwal tare da sanya su aiki a lokaci guda tare da matatun mai na zamani don tabbatar da samuwa da kuma araha a Najeriya.

A cewarsa, ‘yan Najeriya ba za su sami dalilin da zai sa su fuskanci karancin man fetur ba, ganin cewa za a sayar da litar man a kan Naira 100 a lokacin da yake shugaban kasa.

“Man fetur shine abin da Allah ya barwa Najeriya ta ci moriyarsa amma shugabanni sun kwace muku shi sun sanya shi ya yi tsada har ma da talakawa.

“Za mu sayar da man fetur a kan Naira 100 kan kowace lita, mai yiwuwa ne. Za mu gyara dukkan matatun tare da sanya su aiki, sannan za mu gina matatun mai na zamani a kowace shiyyar siyasa ta Kasa.” Inji shi.

Nwanyanwu ya kuma yi alkawarin yaki da rashin tsaro da ya tilastawa mutane barin gonakinsu tare da mayar da mutane gonakin su ci gaba da gudanar da ayyukansu na noma domin tabbatar da wadatar abinci a kasar.

Ya kara da cewa, “A yau, Najeriya za mu gina kuma za mu dawo da amana a Najeriya, za mu tabbatar da cewa an samu takin zamani da kuma araha ga manoma a lokacin shugabancina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *