Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a jihar Akwa Ibom dake kudu maso kudancin Najeriya ta ce hukumar ta shirya wa zaben na ranar Asabar kuma an baiwa kowane ma’aikacin wucin gadi takardar shaidar zama dan takara da tags.
Hukumar zabe (INEC) ta tabbatar da cewa an samar da matakan tabbatar da gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya lami lafiya a jihar Akwa Ibom.
A zantawarsa da Wakilin Muryar Najeriya, Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Odaro Aissien, ya ce duk wani abu mai muhimmanci yana nan a wurin kuma a shirye su ke don rabawa.
Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaron da ke aiki a hukumar suna nan a kasa, domin tabbatar da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da luma
A halin da ake ciki, wasu ‘yan asalin jihar da suka zanta da Muryar Najeriya, sun bayyana cewa a shirye su ke, don kada kuri’a su
Babban birnin kasar, Uyo yana cikin kwanciyar hankali yayin da yawancin mazauna yankin suka matsa kusa da rumbun kada kuri’unsu don tabbatar da kusanci da kuma shirye-shiryen zaben.
‘Yan asalin jihar Akwa Ibom za su bi sahun sauran ‘yan Najeriya mazauna jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja domin zaben sabon shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin kasar ranar Asabar.
Adadin wadanda suka yi rajista a zaben na bana ya kai adadadin miliyan 2,357,418 wanda ya kunshi kashi 41.8% mata da 51.9 maza masu kada kuri’a.
Za a gudanar da zaben ne a dukkan kananan hukumomi 31 da jimillar rumfunan zabe 4,354 da za a kada kuri’a kamar yadda INEC ta nuna.
Leave a Reply