Dan takarar jam’iyyar Labour Party, Mista Obi Aguocha ya samu kuri’u 48,199 inda ya kayar da kakakin majalisar dokokin jihar Abia, Mista Chinedum Orji na jam’iyyar PDP a zaben mazabar Ikwuano, Umuahia ta arewa da Umuahia ta kudu a ranar Asabar.
Orji ya samu kuri’u 35,195 a sakamakon da jami’in mai kula da masu kada kuri’a, FarfesaUma Oke ya sanar a ranar Litinin.
Orji dan tsohon Gwamna ne, Theodore Orji.
Farfesa Oke ya ce Mista Ogbonnaya Obilor na jam’iyyar All Progressives Congress, APC ya samu kuri’u 4,042, yayin da Mista Ogbonna Abariukwu na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance APGA ya samu 2,758, Mista Obinna Nwosu na African Democratic Congress, ADC, ya samu 2386, da Mista Friday Chimaobi na jam’iyyar. Jam’iyyar Young Progressive Party, YPP ta samu kuri’u 1013.
Sauran wadanda suka hada da Patience Okorie na New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta samu kuri’u 644, Mista Christian Ibekwe Christian na National Rescue Movement, NRM, ya samu kuri’u 68 yayin da Mista Nnamdi Ogbuagu na jam’iyyar All People’s Party, APP ya samu kuri’u 347.
Farfesa Oke ya shaidawa manema labarai cewa suna jiran sakamakon zaben karamar hukumar Osisioma domin bayyana sakamakon zaben Sanatan Abia ta tsakiya.
Umuahia ta arewa, Umuahia kudu, Ikwuano, Osisioma, Isiala Ngwa ta kudu da Isiala ta arewa su ne kananan hukumomi shida a gundumar Abia ta tsakiya.
Leave a Reply