Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a jihar Akwa Ibom ta kudu maso kudancin Najeriya ta sanar da Mr Okpolupm Ette na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Eket da aka gudanar a zaben da ya gabata a ranar Asabar.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin jami’in kula da zaben Farfesa Isongesit Solomon a ofishin INEC da ke karamar hukumar Eket a Akwa Ibom.
Solomon, jami’in zabe na karamar hukumar Eket, Ibeno da Onna, ya bayyana Mista Okpolupm Ette na jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP, wanda ya samu kuri’u 33,001 yayin da Mista Eseme Eyibo na All Progressive Party, APC, ya samu kuri’u 16,909.
Leave a Reply