Take a fresh look at your lifestyle.

Ministan Kimiyya, Fasaha Ya Shiga Takarar Shugaban Kasa

0 458
Yayin da wasu ‘yan takarar shugaban kasa suka bayyana sha’awarsu ta tsayawa takarar kujera ta daya a Najeriya, ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Dr Ogbonna Onu, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Da yake bayyana aniyarsa ta zama shugaban kasa, Dr Onu ya ce dole ne Najeriya ta kasance mai dogaro da kanta domin tana da abin da ake bukata domin ta zama mai samar da kayayyaki maimakon ci gaba da zama kasa mai amfani.

Ya ce Najeriya ba za ta kara dogara ga sauran kasashe wajen magance matsalarta ba.

A maimakon haka, zai yi amfani da ilimin tattalin arzikin da kimiyya da fasahar kere-kere ke tafiyar da shi wajen ganin kasar ta yi fice idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *