An Bukaci Jam’iyyun Adawa Su Hada Kai Da Zababben Shugaban kasa Domin Ciyar Da Najeriya Gaba
Abdulkarim Rabiu, Abuja
An Bukaci Jam’iyyun Adawa Su Hada Kai Da Zababben Shugaban kasa Domin Ciyar Da Najeriya Gaba.
Babban daraktan sashen tallafawa al’umma na gangamin yakin neman zaben zababben shugaban kasa Alhaji Ahmed Abdullahi da aka fi sani da AA Mai Agogo shi ya yi kiran yayin da ya ke tsokaci Kan sakamakon zaben shugaba kasa da aka gudanar.
Alhaji Ahmed bayyana zaben da ya gabata a matsayin mafi zaman lafiya idan aka kwatanta da zabubbukan baya, kana ya yi imanin cewa Ja’amar kasa sun yi kyakkyawan zaben shugaban kasa mai hangen nesa da kykkyawan jagoranci ga Alumma tare da kishin ciyar da kasa gaba.
A don haka ya shawarci daukacin ‘yan Najeriya masu kishin kasa su rubanya kokarinsu wajen ganin wannan nasara ta haifarwa kasar da mai Ido.
Kazalika ya shawarci magoya bayan jam’iyyar su zage damtse a zaben gwamnonin dake tafe domin sabuwar Gwamnatin ta sami damar samarwa jama’ar kasa roman Dumukradiyya yadda ya kamata a dukkan jihohin kasar.
Sai daikuma Alhaji AA Mai Agogo ya ja hankalin jamiyyun adawa su hadiye hushinsu su, domin aiki da sabuwar Gwamnatin don ci gaban kasa ba kokarin mai da Kasar baya ba, ta hanyar shiga kotuna.
Baya ga wannan ya tunatar da su cewa zuwa kotu ba abin da zai haifar illa koma baya a kokarin da sabuwar gwnatin za ta yi wajen tabbatar da ci gaban kasa yadda ya dace da tsarin Dumukradiyya.
Dangane da Zabukan gwamnoni dake tafe kuwa, Alhaji AA Mai Agogo ya jaddada kudurin jam’iyyar na yin abin da ya dace, yana mai rokon daukacin ‘Yan jamiyyarsu fito kwai da kwarkwata wajen wannan zaben.
AK
Leave a Reply