Take a fresh look at your lifestyle.

Firaministan Pakistan ya bayyana bakin cikinsa game da asarar rayuka da aka yi a kasar Afganistan Sakamakon Ambaliyar Ruwa

0 420
Pakistan ta bayyana bakin cikinta tare da jajantawa Afganistan dangane da mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a larduna goma na kasar, wanda ya yi sanadin asarar rayuka masu daraja da asarar dukiyoyi.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta ce, firaministan Pakistan Shahbaz Sharif shi ma ya bayyana goyon bayansa ga gwamnatin rikon kwarya ta Afghanistan da kuma al'ummar kasar, tare da mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu da kuma wadanda abin ya shafa.

Firayim Ministan ya sanar da cewa Pakistan na aikewa da agajin gaggawa ga 'yan Afganistan da ambaliyar ruwa ta shafa.

Sanarwar ta ce "Muna tare da mutanen Afganistan a cikin wannan sa'a mai wahala kuma za mu ba su duk wani taimako."

Sharif ya kuma yi kira ga kasashen duniya, musamman ma Majalisar Dinkin Duniya, da su taimaka wa ‘yan Afghanistan da suka rasa matsugunansu, ta hanyar samar da abinci, da taimakon magunguna, da matsuguni.

Ambaliyar da aka yi a baya-bayan nan, a cewar firaministan kasar, na iya dagula yanayin jin kai na Afghanistan.

Jami'an kasar Afganistan sun fada a jiya Alhamis cewa, mutane 8 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu 13 suka jikkata sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu sassan arewacin Baghlan da yammacin Afghanistan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *