Take a fresh look at your lifestyle.

2023: MINISTAN KIMIYA DA FASAHA YA TSAYA TAKARAR SHUGABAN KASA

0 249

A yayin da ‘ yan Takara ke kara nuna shaawar su ta tsayawa Takarar shugabancin Najeriya,shi ma Ministan Kimiya da fasaha, Dr Ogbonna Onu, yanuna shaawar shi ta tsayawa takarar shugabancin kasar a babban zaben da zaa gudanar a Najeriya.

 

Da yake nuna shaawara shi ta tsayaa takara, Dr Onu yace dole a dogara da kai a Najeriya a bangaren kirkira a maimakon shigowa da kayayyaki daga kasashen waje.

 

Sai dole mun samar da kayayyaki masu dimbinyawa kafin kasar taaci gaba domin anfanin mu. Haka kuma muna da duk abunda ya dace na cimma waannan buri. Saboda muna iya samar da abunda zai kawo wa kasar ci gaba domin kawar da talauci, da kuma kara a kasar martaba a idon duniya,” a cewar Dr Onu .

 

Yace Najeriya ba zata ci gaba da dogare da wasu kasashen duniya  domin shawo kan matsalar ta ba.

 

A maimakon hakan, zaiyi anfani da kwarewar shin a bangaren kimiya da fasaha domin bunkasa tattalin arzikin kasar idan har aka zabe shi shugaban Najeriya.

 

Muna da duk abunda ya wajaba domin shawo kan matsalolin mu ba tare da mun gayyato wasu daga sauran kasashe ba. Wannan itace hanyar da ta dace na samar da kimiya da fasaha,kuma ina da yekinin cewa wata rana Najeriya zata zama abun koyi a idon duniya,” inji Dr Onu .

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *