Take a fresh look at your lifestyle.

‘ YAN TAWAYEN CHADI SUNKI KARIN WAADI

0 286

‘Yan tawayen Chadi na tattaunawa a Qatar tare da hukumomin kasar chadin domin cimma yerjejeniyar zaman lafiya sakamakon janye tattaunawar da aka shirya a birnin N’Djamena.

Sunki amincewa da shi saboda abunda suke ganin “tafiyar ahawainiya ne na tsawaita waadin” kamar yadda sanarwar ta bukata wucin gadin daga bakin rundunar soji ne.

Birnin N’Djamena ya amince da nashi yerjejeniyar a ranar Lahadi da aka tsayar tun farko domin gudanar da taron ranar 10th ga watan Mayu, ba tareda sabbin ranaku ba na mika Mulki ga  hannun farar hula.

An dai dauki matakin ne a saboda mahukumtar birnin Qatar dake shiga Tsakani sun bukaci hakan “dan kwarya kwaryar tattauanawa” da yaki ci yaki cinyewa watanni da dama tsakanin kungiyoyin tawaye daban daban.

“Kungiyar sojoji ‘ yan siyasa sunyi naam da matakin da hukumomin Qatar suka dauka” game da dage tattaunawar, kungiyoyin tawayen a cikin wata sanarwar su sun nuna rashin gamsuwar su akan kara waadin rikon kwarya suka ce zai  “bada damar kara waadin a ganin su”.

Kwanaki kadan bayan juyin mulkin da sojoji sukayi a watan Afirilu 2021, kungiyar da ‘ dan tsohon shugaban kasar ke yiwa jagoranci Mahamat Idriss Déby Itno, ya sanar da cewa rikon kwarya na waadin watanni 18 zaa iya kara yawan shi

Haka kuma kungiyoyin tawayen sun bukaci “sanya hannun dukakknin bangarorin siyasar na amincewa da sabuwar ranar waadin rikon kwaryar”.

Wannan  “yar kwarya kwaryar tattaunawar birnin Doha ”, ya baiwa ‘ yan bindiga hamsin dauke da makamai alkawarin watanni da tun farko aka sa ran gudanarwa ranar 27th ga watan Feburairu zuwa  13 ga watan Maris.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *