Take a fresh look at your lifestyle.

Dubban Magoya Bayan Jam’iyyar PDP Sun Koma Jam’iyyar APC A Jihar Katsina

Kamilu LawaL,Katsina

0 235

Sama da magoya bayan jam’iyyar PDP dubu goma (10,000) ne a jihar Katsina dake arewa maso yammacin najeriya suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP tare da bayyana goyon bayan su ga jam’iyyar APC mai mulkin jihar

 

 

Mabiyan sama da dubu goma sun komo jam’iyyar ta APC bisa nuna goyon bayan su ga wasu jiga jigan jam’iyyar PDP da suka yanke shawarar marama dantakarar gwamnan jihar kalkashin jam’iyyar APC Dr. Dikko Radda baya domin ganin ya samu nasara a zaben gwamnonin jihohi wanda hukumar zaben kasar INEC) zata gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Maris da muke ciki a jihohin kasar.

 

 

Tsaffin Jiga jigan da suka baro jam’iyyar ta PDP zuwa APC wadanda gwamnan jihar Aminu Masari ya karbe su a gidan gwamnatin jihar sun kunshi mutane bakwai na hannun damar tsohon gwamnan jihar kalkashin jam’iyyar PDP Ibrahim Shema

 

 

Daga cikin su akwai tsohon sakataren jam’iyyar PDP na shiyyar arewa maso Yamma, Bashir Tanimu Dutsinma da tsohon shugaban Kungiyar shugabannin  kananan hukumomi(ALGON) kuma tsohon shugaban karamar hukumar Kaita Ibrahim Lawal Dankaba da kuma wasu jigan siyasar PDP da wani hamshakin dan kasuwa kuma na hannun damar tsohon gwamnan jihar Ibrahim Shema, Alhaji Idris Kwado da sauran wasu daga cikin jiga jam’iyyar PDP a jihar

 

 

Da yake wa taron manema labarai jawabi, babban darektan kwamitin yakin neman zaben dantakarar gwamnan jihar kalkashin jam’iyyar APC Arch. Ahmad Dangiwa ya bayyana cewa samun goyon bayan yayan jam’iyyar ta PDP wadanda suka dawo jam’iyyar ta APC wata babbar alama ce dake nuna cewa a jihar Katsina jam’iyyar APC ce zata lashe kujerun a zaben gwamnan jihar da na Yan majalisun da hukumar zabe ta kasa (INEC) zata gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Maris da muke ciki

 

 

Kazalika, masu sharhi akan lamurran siyasa a jihar ta Katsina na da amannar cewa shigowar jama’ar tsohon gwamnan jihar Ibrahim Shema a jam’iyyar ta APC manuniya ce dake nuni da cewa dantakar jam’iyyar APC ya samu goyon bayan tsohon gwamnan Ibrahim Shema al’amarin kuma dake nuni da cewa baya goyon bayan dantakar jam’iyyar PDP Yakubu Lado Danmarke wanda suke jam’iyya daya kafin faruwar wannan lamari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *