Rahotanni na cewa, shugaba Xi Jinping ne ya nada Li Qiang a matsayin firaministan kasar Sin na gaba kuma majalisar dokokin kasar ta zabe shi a hukumance.
Li Qiang, tsohon shugaban jam’iyyar gurguzu na birnin Shanghai mafi girma a kasar, yanzu zai jagoranci gwamnati, inda ya maye gurbin Li Keqiang mai ritaya.
Dan shekaru 63 ya samu kusan kowacce kuri’a daga wakilai sama da 2,900 a majalisar wakilan jama’ar kasar.
Aboki na Mr. Xi, ana kallonsa a matsayin mai fafutuka, kuma za a dora masa alhakin farfado da tattalin arzikin kasar Sin da ke fama da yamutsi.
A halin da ake ciki kuma, ana sa ran za a bayyana sabbin nade-naden mukaman ministoci ranar Lahadi.
Ba a ba wa ‘yan jarida damar shiga dakin ba yayin da ake kada kuri’a.
Mr. Li, wanda yanzu shi ne babban jami’i na biyu mafi girma a tsarin siyasar kasar Sin, ya samu kuri’u 2,936, inda wakilai uku kacal suka kada kuri’ar kin amincewa da nadin nasa, takwas kuma suka kaurace.
Daga nan sai ya yi rantsuwa, yana mai rantsuwar kasancewa mai biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar Sin, da kuma “yin aiki tukuru don gina kasa mai ci gaba, mai karfi, da dimokuradiyya, da wayewa, mai jituwa, mai girma na gurguzu na zamani.”
Nadin nasa ya zo ne bayan da Mr. Xi ya samu wa’adi na uku mai tarihi a matsayin shugaban kasa a ranar Juma’a.
Ko da yake, tun daga Mao Zedong, shugabannin kasar Sin sun takaita wa’adi biyu ne kawai. Lokacin da Mr. Xi ya sauya wannan takunkumin a shekarar 2018, ya mayar da shi wani mutum wanda ba a taba ganin irinsa ba tun lokacin da shugaba Mao ya yi.
Leave a Reply