Take a fresh look at your lifestyle.

Kenya ta kulla yarjejeniyar Mai da UAE da Saudiyya

Maimuna Kassim Tukur,Abuja.

91

Kenya ta kulla yarjejeniya da Kanfanonin ADNOC ta UAE da Saudi Aramco don samar da kayayyakin man fetur tare da bada bashi na watanni shida.

 

 

Ministan makamashin kasar ya ce an yi hakan ne domin dakile bukatar dalar da ta durkusar da kudaden kasar.

 

 

Ministan Makamashi Davis Chirchir ya shaida wa taron manema labarai a ranar Juma’a cewa an sanya hannu kan yarjejeniyoyin biyu daga wasu kamfanoni bakwai.

 

 

‘Yan kasuwar kasashen waje sun nuna shakku kan yiwuwar shirin na dakile matsin lamba kan kudin Shilling, inda suka ce hakan ya yi daidai da dage bukatar da ake yi.

 

 

Haka kuma wasu masu shigar da kara masu zaman kansu suna kalubalantar shirin a babban kotun.

 

 

Rahoton ya ce a ranar Talata ne ake sa ran kotun za ta bayar da umarnin farko kan lamarin.

Comments are closed.