Take a fresh look at your lifestyle.

Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Ba Da Gudummawar Asibiti Ga Al’ummar Kishi Dake Jihar Oyo

0 135

Shugaban hafsan sojin kasa (COAS) Laftanar Janar Faruk Yahaya ya kaddamar da wani babban asibitin gadaje 60 na zamani a babban asibitin Kishi dake karamar hukumar Irepo a jihar Oyo.

 

 

Dukkanin al’ummar sun cika da murna da jinjina ga rundunar sojojin Nijeriya (NA) bisa samar da cibiyar kiwon lafiya da hukumar ta gina tare da samar da cikakken kayan aiki.

 

Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce, wurin ya kunshi dakunan mata da maza, dakunan yara, dakin aiki, ofisoshin Likitoci, wurin jinya da kuma wurin karbar baki.

 

 

Da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin, COAS ya bayyana aikin a matsayin daya daga cikin ayyukan sa na musamman na hadin gwiwan soja na farar hula da ke da nufin lashe zukata da tunanin ‘yan Najeriya ta hanyar samar da ababen more rayuwa.

 

Ya jaddada cewa sojojin Najeriya na ‘yan Najeriya ne don haka dole ne su hada kai wajen tabbatar da cewa Najeriya ta kasance cikin kwanciyar hankali da tsaro.

 

 

Hakazalika, COAS din ya bayyana godiyarsa ga kwamandan rundunar sojin Najeriya, Shugaba Mohammadu Buhari bisa goyon bayan da yake baiwa hafsoshi da sojojin na NA.

 

Hadin kan kasa

 

 

Gwamnan jihar Oyo, Engr. Sheyi Makinde wanda ya samu wakilcin Hon Lateef Adediran, ya yabawa hukumar ta NA bisa yadda take taimaka wa hadin kan kasa da zaman lafiya a duniya ta hanyar ayyukan tsaro na cikin gida da kuma gudunmuwar da sojoji ke bayarwa ga ayyukan tallafawa zaman lafiya.

 

Ya kuma yabawa rundunar a madadin gwamnati da al’ummar jihar Oyo bisa zabar Kishi domin gudanar da aikin abin yabawa.

 

 

Da yake bayyana dalilin da ya sa aka zabar dakunan asibitocin al’ummar Kishi, mai gudanar da aikin, Manjo Janar Kunle Adesope wanda shi ne shugaban asusun ajiya da kasafin kudi; wani dan Kishi, ya nuna cewa zabin da ya zaba na asibitocin jama’arsa ya dogara ne akan tantance bukatu, tuntubar shugabannin al’umma da kuma fadin cewa “lafiya ita ce arziki”.

Sauran manyan baki da suka halarci taron sun hada da HRM, Iba na Kishi, Oba Moshood Oyekola Lawal, shugaban iyalan Adesope, Cif Bayo Adesope, manyan hafsoshi daga hedikwatar tsaro da sojoji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *