Take a fresh look at your lifestyle.

Sabuwar Dokar Muhalli Ta Taimaka Wajen Yaki Da Covid-19: Dr Yakubu

Musa Aminu, Abuja

162

Mahukunta a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakunansu kan cika shekaru uku da bullar cutar korona cikin kasar.

Shugaban Hukumar Duba-gari ta kasar, Dakta Yakubu Muhammad Baba ya bayyana yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karfafa ayyukansu ta hanyar sanya hannu a sabuwar dokar kula da muhalli a Najeriya, da kuma yadda ta sauya fasalin ayyukan kula da muhalli tare da irin gudummawar da suka bayar wajen dakile cutar tun bayan bullarta a ranar 27 ga watan februrun shekarar 2020.

Dakta Yakubu Muhammad ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a Abuja babban birnin kasar, ya kuma kara da cewa,’’Kamar dai yadda ka yi magana, mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin yanayin tsare-tsaren gyaran mulkinsa, a ranar 6 ga watan Agusta na shekarar da ta gabata ya sa hannu a sabuwar doka da ta gyara fasalin ayyukan mu na Duba-gari a Najeriya baki daya. Hakan ya sanya muka canza suna; a da abin da dokar mu ta kayyade shi ne mu yi rijista ga ma’aikatanmu da suke aiki a fadin Nijeriya. Sannan mu tsara musu dokokin yanayi na koyarwa da fahimtarwa da yadda za su yi aikinsu. To shugaban kasa ya canza mana suna kuma ya kara mana abin da Bature yake cewa ya yi ‘Strengthening’ aikin duba gari a Nijeriya inda ya sanya hannu a sabuwar doka”.

Dangane da batun da ya shafi kakkabe annobar korona a Najeriya kuwa ya ce “Ka san shi aikin lafiya akwai mataki-mataki. Da ‘guidelines’ da yake tattare da shi. Ita hukumar lafiya ta duniya wato WHO, ita take da alhakin sakin matakan dauka na tursasawa kan wannan koronabairos din. Idan ku ka lura shekara ta farko da ta biyu babu wani mataki mai sassauci da ya fito daga hukumar lafiya ta duniya, saboda annobar tana kan ganiyarta. Lokacin da aka fara samun sauki sai aka fara saukaka kayyadewa. Misali; masu fita kasashen waje idan ka zo sai an yi maka gwajin korona a tashar jirgin sama, an tabbatar ba ka da korona. Daga bisani Kuma aka zo aka fara saukaka kayyadewan, aka ce da zarar kana da sahihin shaidar cewa an yi maka allura, zaka iya tafiya. Idan ka je ba ka da bukatar gwajin kana da shi ko baka da shi, wannan shi ne matakin da muke ciki a halin yanzu. Saboda da farko da zarar ka sauka a Nijeriya, kana da bukatar ka cike wasu takardu, za ka biya kudin gwaji a tashar jirgin saman, za su kyale ka tafi tare da bibiyar inda kake, sannan idan akwai wani rahoto, cikin sauki za su je wurin su dauke ka zuwa muhallin killace masu dauke da annobar, wannan yana nufin a wancan lokacin korona na kan ganiyarta.”

Daga karshe ya shawarci al’umma da su ci gaba da yin duk abin da suka san za su iya yi na kariyar kai, sannan abu mafi muhimmanci kowa ya tabbatar da cewa ya je ya karbi rigakafin korona, saboda idan ka karbi wannan rigakafin korona din zai taimaka.

Ba wai ana cewa idan ka karbi rigakafi ba za ka yi korona ba ne, a’a ko da korona za ta kama ka za ta zo da sauki.

Ya kuma jaddada bukatar dake akwai wajen ganin al’umma sun ci gaba da daukan matakan nan na (self medication) wato bada tazara da wanke hannaye da kauracewa cunkoson jama’a da dai sauransu.

AK

Comments are closed.