Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamna Ganduje ya kafa kwamiti kan gobarar Kasuwar Kurmi da Singer

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

0 256

Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya ya ziyarci wuraren da aka samu iftila’in gobara a kasuwannin Kurmi da Singer da ke a tsakiyar birnin Kano inda ya jajantawa al’ummar da suka fuskanci wannan jarrabawa.

 

 

Yayin ziyarar  Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa kwamiti mai mambobi 11 don nazari kan bala’in gobarar da ta lalata dukiyoyi a sashen ‘yan leda na tsohuwar kasuwar mai dinbin tarihi ta Kurmi, da ma shagunan da gobarar ta lakume a saman ginin tsohon bankin Savannah da ke a kasuwar  Singer.

 

 

A jawabin da ya fitar kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Malam Muhammad Garba yace, “an dora wa kwamitin alhakin gudanar da bincike kan musabbabi na aukuwar gobarar  da ma ba da shawarwari kan hanyoyi da za a bi don kaucewa sake afkuwar bala’in gobarar nan gaba”.

 

 

Har ila yau ya kara da cewa kwamitin zai samu jagoranci ne na kwamishinan kasuwanci da masana’antu da kungiyoyin gama kai da albarkatun kasa  Barista Mukhtar Ibrahim wanda kuma zai mayar da hankali kan duba irin asarar da aka yi da ba da shawarwari kan hanyoyi da gwamnati za ta ba da tallafi ga ‘yankasuwar da iftila’in ya shafa.

 

 

Mambobin kwamitin sune, Alhaji Sabi’u Bako da Malam Muhammad Garba kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida da Alhaji Uba Zubairu Yakasai, shugaban kasuwar Abubakar Rimi (Sabon Gari).

 

 

Sauran kuwa sune; Alhaji Tijjani Jiyali shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da ke Gidan Savannah kasuwar Singer da Alhaji Ya’u Idris Karas shugaban kungiyar ‘yankasuwa ta kasuwar Kurmi da Alhaji Bature Garkuwa shugaban kwamitin amintattu na kungiyar kasuwar ta Kurmi da  Alhaji Auwalu Anyayo shugaban kungiyar masu siyar da Citta kasuwar Kurmi  da Alhaji Ya’u Adamu,shugaban ‘yan ksuwa masu harkar leda a kasuwar ta Kurmi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *