Take a fresh look at your lifestyle.

Sakataren Amurka Ya Ziyarci Habasha Da Nijar

Maimuna Kassim Tukur,Abuja.

0 114

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya kai ziyara Nahiyar Afirka domin wani rangadi na kasashe biyu na baya bayan nan a jerin ziyarar da manyan jami’an Amurka suka kai nahiyar.

 

 

Tsaro, da bala’in fari, da kuma barazanar masu jihadi a yankin Sahel ne za su mayar da hankali kan ziyarar Mr. Blinken a kasashen biyu a wannan mako.

 

 

A ranar Laraba ne zai je kasar Habasha domin tattaunawa kan aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hannu tsakanin gwamnati da dakarun ‘yan tawaye bayan yakin da aka kwashe shekaru biyu ana yi.

 

 

Zai kuma gana da hukumomin jin kai a kasar.

 

 

Kasar Habasha na fama da sakamakon yakin da ya raba dubban mutane da matsugunansu da kuma illar fari mafi muni a yankin kahon Afirka cikin shekaru da dama.

 

 

Sakatare Blinken zai ziyarci Nijar a karon farko da wani sakataren harkokin wajen Amurka zai kai ziyara, kuma zai taimaka wajen kara kaimi wajen dakile yaduwar kungiyoyin masu jihadi a yankin Sahel.

 

 

Ziyarar tasa a Afirka ta biyo bayan na uwargidan shugaban kasar Amurka Jill Biden, wadda a watan jiya ta ziyarci Namibiya da Kenya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *