Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da mambobin hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta ICPC guda bakwai.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa da ke Abuja da safiyar Laraba.
Wadanda aka rantsar sun hada da Mai Shari’a Adamu Bello (Jihar Katsina); Hannatu Mohammed (Jihar Jigawa); Olubukola Balogun (Lagos); Obiora Igwedibia (Jihar Anambra); Dr. Abdullahi Saidu (Jahar Niger); Yahaya Dauda (Jihar Nasarawa) da Grace Chinda (Jahar Ribas).
Bikin rantsar da su ya kasance gabanin fara taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta Tarayya.
A halin yanzu, shugaba Buhari yana jagorantar taron majalisar ministocin a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.
Sauran sun hada da ministocin ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, kudi, Zainab Ahmed, harkokin mata, Pauline Tallen da na babban birnin tarayya, Mohammed Bello da dai sauransu.
Leave a Reply