Take a fresh look at your lifestyle.

Infantino Ya Samu Sabon Wa’adin Shekaru Hudu A Matsayin Shugaban FIFA

243

An sake zaben Gianni Infantino a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA).

 

 

KU KARANTA KUMA: Shugaban FIFA zai sake yin wa’adin shekaru hudu

 

 

An gudanar da zaben ne a ranar Alhamis yayin babban taro karo na 73 da aka yi a Kigali, yayin da Infantino ya tsaya ba tare da hamayya ba, lamarin da ya sa sake zabensa a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya.

 

 

Rigingimun da suka dabaibaye shi sun hada da, yadda ake yiwa ma’aikatan bakin haure a gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a bara da kuma gazawar shirin buga gasar duk bayan shekaru biyu.

 

 

Infantino, duk da haka, ya yi alkawarin samun rikodi na kudaden shiga a cikin shekaru hudu masu zuwa na dala biliyan 11 yayin da ya yi kira da a kara buga kwallon kafa a duniya.

 

 

“Abin alfahari ne mai ban mamaki da gata, kuma babban nauyi ne.

 

 

“Na yi alkawarin ci gaba da yi wa FIFA hidima da kwallon kafa a duniya.

 

 

“Ga wadanda suke so na, kuma na san akwai da yawa, kuma wadanda suka ƙi ni, ina son ku duka,” a cewar infantino.

 

 

Infantino ya tabbatar da samun kudin shiga na FIFA ya kai matakin rikodi a zagayen karshe na shekarar 2019-2022, amma ya yi alkawarin sake farfado da hakan a bayan fafatawar gasar cin kofin duniya ta maza da mata da kuma gabatar da gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi 32.

 

 

“Kudaden shiga sun karu zuwa dala biliyan 7.5 (zuwa 2022) a cikin lokacin da COVID-19 ya shafa.

 

 

“Lokacin da na isa, asusun FIFA ya kai kusan dala biliyan 1, a yau sun kai kusan dala biliyan 4,” infantino ya ce.

 

 

“Mun yi alkawarin sabbin kudaden shiga na rikodi na dala biliyan 11 na gaba, kuma ba a sanya sabon gasar cin kofin duniya a cikin wannan adadi, don haka zai iya karuwa da biliyan biyu (fiye).

 

 

A shekarar 2016 ne aka fara zaben Infantino a wata babbar majalisa bayan murabus din Sepp Blatter wanda ya gada, kuma ya ci gaba da rike mukaminsa ba tare da hamayya ba bayan shekaru uku.

 

 

Amma wannan ya kasance a matsayin wa’adin mulki na biyu don haka zai kasance a karo na uku kuma na karshe a cikin shekaru hudu.

Comments are closed.