Take a fresh look at your lifestyle.

Tsoffin Sojojin Habasha Daga Tigray A Sudan Domin Samun Mafaka

0 457
Wasu tsaffin dakarun wanzar da zaman lafiya 40 da suka fito daga yankin Tigray da ke fama da yakin Habasha sun isa gabashin Sudan bayan neman mafaka.

A watan da ya gabata, sama da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya 500 da aka girke a yankin Abyei da ake takaddama a kai tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, sun nemi birnin Khartoum, saboda fargabar tsaron lafiyarsu idan za su koma gida.

Wani jami'in hukumar 'yan gudun hijira ta Sudan ya tabbatar da cewa daruruwan dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Habasha sun nemi mafaka bayan kammala aikinsu a Abyei.

"Isowar masu neman mafakar za su ci gaba da tafiya a kullum har sai an kwashe su duka," in ji jami'in, wanda ya yi magana kan yanayin.

Tsoffin dakarun wanzar da zaman lafiya da suka isa ranar Lahadi an kai su sansanin ‘yan gudun hijira na Um Gargour da ke gabashin Sudan.

Tun bayan da Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai daga Sudan a shekara ta 2011 ne ake gwabza fada a yankin Abyei.

Majalisar Dinkin Duniya ta kafa aikin wanzar da zaman lafiya a waccan shekarar, kuma tun a wancan lokaci ta tura dakaru kusan 4,000 musamman Habashawa zuwa yankin.

A watan da ya gabata, ma'aikatar tsaron Habasha ta ce dakarun wanzar da zaman lafiya daga Tigray da suka ki komawa, sun kasance wadanda " farfagandar 'yan tawaye suka fuskanta.

Dakarun wanzar da zaman lafiya ‘yan kabilar Tigrai da aka yi hira da su, duk sun ce sun damu da tsaron lafiyarsu, inda wani babban jami’i ya ce an kama wasu ko kuma aka kashe wasu da suka dawo daga Habasha.

Yakin arewacin Habasha ya barke ne a watan Nuwamban shekarar 2020, lokacin da Firayim Minista Abiy Ahmed ya aike da sojoji zuwa yankin Tigray a matsayin martani ga harin da 'yan tawaye suka kai kan sansanonin sojoji.

A shekarar da ta gabata, kusan tsoffin dakarun wanzar da zaman lafiya 120 'yan kabilar Tigrai da aka tura a yankin Darfur sun nemi mafaka a Sudan, a cewar MDD.

Kasar Sudan ta karbi dubun dubatan ‘yan gudun hijirar Habasha tun bayan barkewar rikicin na Tigray.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *