Take a fresh look at your lifestyle.

SARKIN KANO YA TAYA ABBA KABIR MURNA

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

35

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP ya taya Zabbben Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf Murna bisa nasarar da ya samu ta lashe zaben Gwamnan Kano a zaben da aka gudanar ranar Asabar din data gabata 18th ga wannan wata na Maris.

 

Cikin wata sanarwa daga Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa ta bayyana cewa al’ummar kasar nan sun karbi tsarin mulkin damokaradiyya da matuqar muhimmacin idan akayi la’akari da yadda suka futo domin jefa kuri’unsu kamar yadda tsarin mulki ya bada dama.

 

 

Sanawar ta kuma godewa malamai da Limamai da sauran Al’umma bisa addu’ar zaman lafiya da suka dunga yi kafin da kuma bayan gudanar da zaben.

 

 

Daga nan fadar Masarautar ta Kano tayi nasiha tare da kira ga sabon gwamnan daya hada kai da dukkanin rukunin al’umma wajen tafiyar da gwamnati, domin yin hakan zai taimaka wajen kyautata rayuwar al’umma da kuma kawo cigaban da ake bukata domin bunkasar tattalin arziki ga jihar Kano da kasa baki daya

Comments are closed.