Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Jihar Neja da karamar hukumar Bargu zasu sake gina gadar Babanna

Nura Muhammed,Minna.

182

Gwamnatin jihar Neja zata hada hannu da karamar hukumar Bargu domin sake gina gadar Babanna da ta hade jahar Neja da jamhuriyar Benin don Kara bunkasa Kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

 

 

Shugaban karamar hukumar Bargu Alhaji Suleiman Yarima shine ya bayana hakan a lokacin da yake zantawa da muryar Najeriya a Minna fadar gwamnatin jahar Neja arewa ta tsakiyar Najeriya.

 

 

Alhaji Suleiman Yarima ya ce,” gwamnati na ta himmatu wajan ganin ta shinfida ayyukan ci gaba ga a’lummar Karamar hukumar Bargu.

 

 

“gadar da ta hade Najeriya da jamhiruyar Benin tana da mahimmaci musammam yadda take sada alummomin da cinikaiya wanda hakan wani abun cigaba ne ta fannin Kasuwanci a tsakanin kasashen biyu”. A cewar Shugaban Karamar Hukumar

 

 

Alhaji Suleiman Yarima ya ce a lokacin ruwan sama alummar yankin wadanda mafi yawancin  su manoma ne suna wahala sakamakon rubtawar gadar.

 

 

Inda ya ce gwamnatin sa na kokarin ganin an sake gina gadar kafin saukan ruwan sama a wannan shekarar da muke ciki.

 

 

Shugaban karamar hukumar ya Kuma godewa gwamnatin jahar karkashin shugabancin gwamnan Abubakar Sani Bello bisa amsa bukatar sa na sake gina gadar a matsayin wani yunkurin kawowa alummar karamar hukumar Bargu  ayyukan cigaba a jahar Neja.

 

 

A wani labarin kuma shugaban karamar hukumar Bargu Alhaji Suleiman Yarima ya tura tawaga ta musamman domin jajantawa alummar yankin Niganji dake jamhuriyar Benin bisa iftila’in da ya faru da su inda sojoji suka hallaka wasu mutane da suke kan hanyar su ta komawa gida Babanna.

 

 

Shugaban shugabannin kananan hukumomin jihar Neja 25 Alhaji Suleiman Yarima ya bukaci alummar yankin na Babanna da su yi hakuri domin dakarun sojan Najeriya na iyakar kokarin su na ganin sun gudanar da bincike da Kuma hukunta duk Wanda ke da hannu a lamarin.

Comments are closed.