An bukaci masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC reshen jihar Taraba dake Arewa maso gabashin Najeriya da su hada kai da junansu domin ceto jam’iyyar daga halin tsaka mai wuya da ta samu kanta a ciki a jihar.
Dantakarar gwamnan jihar Taraba a inuwar jam’iyyar APC lokacin zaben fitar da gwanin a zaben da ya gabata Chief David Sabo Kente da aka fi sani da DSK shi ne ya yi wannan kiran a lokoacin da yake zantawa da manema labarai dangane da zaben gwamnan jihar ta Taraba da na yan majalisun dokokin jihar da ya gudana ranar goma shatakwas ga watan Maris din nan.
Chief David sabo Kente ya ce babban abun godiya ga Allah shi ne an yi zaben lafiya batare da samun ya mutsi ba, sai dai ya bayyana bukatar dake akwai wajen ganin ‘ya’yan jam’iyyarsu ta APC sun koyi darasi dangane da yadda a ka yi wa jam’iyyar fintikau yayin zaben gwamnan jihar na Taraba da na ‘yan majalisun dokokin jihar.
Sabo Kente ya zargi yadda uwar jam’iyyar ta gudanar da zaben fitar da gawani mai cike da alamun tambaya a matsayin abunda ya haifar da nakasu ga jam’iyyar.
” Mun gode wa Allah, mun gama zabe lafiya Kuma tun da aka gama zabe har aka fidda Sakamakon addu’armu shi ne mu Hada kaimu mu nemi hakuri da juna, a samu a haka Kai don Taraba ta ci gaba” In Chief Devid Sabo
Ya ce rashin adalcin da aka yi a Jam’iyyar APC ne ya sa wasu yayan Jam’iyyar suka fita daga APC, sannan suka zabi Jam’iyyar NNPP da Kuma PDP Mai Mulki.
Kazalika, Jigo a APC a jihar Taraba kuma daya daga cikin wadanda aka fafata da su yayin zaben fitar da gwanin takarar gwamnan jihar ya kara da cewa babban abunda ke gaban duk wani mai kishin jihar yanzu shi ne hada kai domin ciyar da jihar gaba a kuma yi shirin dinke barakar da ya haifar da gagarumin gibi a jam’iyyar kafin zabe mai zuwa.
Ya ce ” ka san idan bau ya faru haka ya kamata a zauna a natsu Kuma a yi bincike a ga mai ya faru. Ai manyan Jam’iyyar sun san abin da ya faru. Kira ga manyanmu shi ne a hada Kai a yi gyara Kuma a yi wa mutane adalcin domin tunkarar zabuka nagaba. Fadace – fadace tsakaninmu shi ya sa muka samu Wannan sakamakon”.
Tuni dai hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta sanar da sunan kanal Agbu Kefas mai ritaya na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar ta Taraba, yayin da dantakarar gwamnan jihar a jam’iyyar NNPP Farfesa Sani Yahya ya zama na biyu dake biye masa a yawan kuri’u, sai Sanata Emmanuel Bwacha na jamiyyar APC da ya zo na uku a zaben.
Abdulkarim Rabiu
Comments are closed.