Take a fresh look at your lifestyle.

Gyaran Hanya:Gwamnan Jihar Kwara Ya Yaba Wa Shugaba Buhari

269

Gwamnatin jihar Kwara ta bukaci mazauna yankin da su rinka kula da tsaftar muhalli domin inganta rayuwa.

 

 

Ma’aikatar muhalli ta jihar ta bukaci al’ummar jihar Kwara da su shiga aikin tsaftar muhalli na wata-wata da kuma hanyar cimma wannan buri.

 

 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Yakub Aliagan, Sakataren Yada Labarai na Ma’aikatar Muhalli.

 

 

Sanarwar ta tunatar da mazauna yankin cewa ana gudanar da aikin tsaftar muhalli a duk wata a ranar Asabar na karshen kowane wata daga karfe 7 na safe zuwa karfe 9 na safe.

 

 

“An umurce ku da ku shiga cikin aikin tsaftar muhalli ta hanyar tsaftace wuraren zama da kasuwancin ku. 

 

 

Sanarwar ta kara da cewa, “Ba za a yi zirga-zirgar ababen hawa da na mutane a fadin jihar ba, tsakanin karfe 7 na safe zuwa 9 na safe a ranar.” 

 

 

Aliagan ya jaddada cewa hukumomin sa ido za su kasance a kasa don tabbatar da bin doka a fadin jihar.

 

 

Ya bayyana cewa, motocin sarrafa sharar za su kasance a kan tituna domin tattara sharar da zubar a wuraren da ake zubar da shara.

 

 

KU KARANTA KUMA: Tsaftar muhalli: Masu ruwa da tsaki sun yi kira da a dauki matakin hana yin bayan gida a fili a Ngeria

Comments are closed.